CUS CUS PLANTAIN
INGREDIENTS
Agada
Ƙwai
Nama
Maggi/Gishiri
Albasa
Citta da sauran kayan kamshi METHOD
Dafarko zaki dafa nama da albasa,citta maggi/gishiri, idan naman ya dahu sai ki dakashi a turmi yadaku sosai ki jiye gefe ɗaya. feraye agadar amma dafaɗi sosai da kuma kauri yadda idan an lanƙwasa bazata karyeba.sai ki ɗauko wannan dakakken naman ɗan kaɗan a hannun ki,sai ki sa shi a tsakiyar plantain ɗin sai a haɗe sama da kasan a soke da tsinken sakace.haka za kiyi tayi har ki gama gaba ɗaya. kada ƙwai a kwano ko ruba zuba maggi da Gishiri,sai arinka ɗaukan wannan agadar ana sawa cikin ƙwan sannan a soya a mai mai zafi.amma ayi a hankali gurin saka naman da kuma tsinken sakacen ɗan kaɗa ya buɗe ko kuma agadar ta yage. Hmmmmm in dai nama ne sai angaji da cinsa